(ABNA24.com) Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS / CEDEAO, ta nemi da a sake gudanar da zaben cike gurbi na ‘yan majalisar dokoki a kasar Mali.
Wannan na kunshe ne a rahoton da tawagar kungiyar ta ECOWAS ta fitar, bayan data ziyarci kasar ta Mali, dake fama da rikice rikice ciki har da na siyasa.
ECOWAS, ta bukaci kotun tsarin mulkin kasar ta Mali, data sake kiran zabe a yankunan da ake ta tada kura kan sakamakon zaben, musamman a yankunan ‘yan adawa da masu mulki suka samu rinjaye.
Zaben cike gibin ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar na daga cikin batun da ya janyo rikicin siyasa a kasar.
A baya baya nan dai ‘yan adawa a Mali, da wasu kungiyoyin fara hula na ci gaba da matsin lamba wa shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita da ya yi murabus sakamakon gazawa.
/129
23 Yuni 2020 - 03:25
Lambar labari: 1049215
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS / CEDEAO, ta nemi da a sake gudanar da zaben cike gurbi na ‘yan majalisar dokoki a kasar Mali.